Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sanya wa wani umarni 11 hannu da zai tabbatar da kula da ofisohsin gwamnati a faɗin ƙasar.
Buhari ya saka hannu kan dokar da ake yi wa laƙabi da Executive Order 11, jim kaɗan kafin fara zaman Majalisar Zartarwa a yau Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Jim kaɗan kafin saka hannun, Buhari ya nemi dukkan ma’aikatun gwamnati, da sashe-sashe, da hukumomi da su kafa sashen kula da tafiyarwa ƙarƙashin sabuwar dokar.
Bayan kammala sa hannun ne Buhari ya jagoranci zaman majalisar, wanda ministoci da sauran ƙusoshin gwamnati ke halarta.