fidelitybank

Buhari ya rusa haramtaccen kwamitin binciken kuɗi

Date:

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan wani ikirari da kwamiti na musamman da shugaban kasar ya kafa domin ya gudunar da bincike a kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki.

Shugaban kwamitin, Gudaji Kazaure ya yi zargin cewa, wasu hukumomin da binciken ya shafa suna kokarin hana ruwa gudu game da aikin nasa, da kuma hana shi ya mika wa shugaba Muhammadu Buhari rahotonsa.

A cewar kwamitin wanda aka dora masa alhakin binciken cajin kudin ajiya da cire kudin tun daga shekara ta 2013 zuwa yanzu, ya gano cewa, babban bankin kasa ya tara fiye da naira tiriliyon tamanin, amma ya yi zargin cewa ana sama da fadi da kudin.

Malam Garba Shehu, shi ne mai magana da yawun shugaban kasa, ya yi karin bayanin kan wannan batun ga BBC.

“Wannan magana ta Gudaji Kazaure ba za a ce kwamiti ne ba. E, ya kafa kwamiti da kansa kuma ya nada jami’ai a ciki har da alkalin alkalan ƙasa da wasu mambobi. Ya sami shugaban kuma ya nuna masa kwato kudade na kasa za a yi.”

Garba Shehu ya ce, duk mutumin da ya gaya wa Buhari cewa zai kwato kudi, zai ce masa Allah-san-barka, sai dai ya musanta cewa shugaban kasa ne ya kafa kwamitin:

“A zahirin gaskiya, duk wanda ya san yadda gwamnati ke tafiya, babu yadda za a ce shugaban kasa a bangaren gwamnati ya kafa kwamiti ya ba wa dan majalisa sakatare, ya kuma kira alkalin alkalai ya nada shi mamba. Ai an yi wa tsarin mulki karen tsaye.

Ya ce kwamiti haramtacce ne, “ba shi da hurumi a doka, shi yasa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a rusa shi, a kuma kafa sabo wanda ke karkashin ministan shari’a.”

Ya kuma bayyana mamakinsa kan yawan kudaden da Gudaji Kazaure ke ambatowa a kalamansa da ke cewa biliyoyin daloli ne aka yi badakkalarsu.

“Wannan zargi na tiriliyan 160 da yake cewa sun salwanta, ina kudin suke? Tiriliyan 160 fa.”

Ya ce idan aka tattara dukiyar da dukkan bankunan Najeriya wuri guda, ba su kai kashi daya cikin uku na kudaden ba.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...
X whatsapp