Shugaba Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan kudurin lafiyar kwakwalwa da aka gabatar tun 2021 bayan da ta kasa tsallake muhawara tun 2003 zuwa 2013.
Majalisun tarayyar ƙasar sun yi muhawara a kan kudurin a 2021.
Shugaban kwamitin harkokin lafiya na majalisar dattawa, Ibrahim Oloriegbe, ne ya tabbatar da amincewa da kudurin da Buhari ya yi a shafinsa na twita.
Kudurin dai zai kare hakkin masu lalurar kwakwala kamar haramta cin zarafinsu a bayar da gidaje da samar da aikin yi da kulawar lafiya da sauran abubuwa.
Har ila yau, kudurin zai tabbatar da ganin cewa masu lalurar kwakwalwa na da damar irin jinya da za a yi musu sannan babu tirsasawa.
Wasu abubuwa da suke kunshe cikin dokar sun haɗa da samar da asusun lafiya na masu lalurar kwakwalwa da kirkiro da sashin lafiya a ma’aikatar lafiya ta ƙasa da kuma kirkiro da kwamitin sa ido kan masu lalurar da sauransu.