Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da tsohon Sifeton ‘yan sanda, Solomon Arase mai ritaya a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda.
Sabon shugaban ya sha rantsuwar kama aiki ne ranar Laraba a fadar gwamnatin da ke Abuja, gabanin fara taron majalisar zartarwa.
Watanni biyu da suka gabata ne dai majalisar dattawa ta amince da shi a matsayin shugaban hukumar.
Solomon Arase wanda ya yi ritaya daga aikin ɗan sanda a shekarar 2016, ya yi aiki a sassa daban-daban na rundunar ‘yan sanda, kafin daga bisani ya zama babban sifeton ‘yan sanda na ƙasa a shekarar 2015.