Ministan ayyuka da gidaje, tsohon gwamnan Legas Babatunde Raji Fashola ya gabatar da takardun gidaje ga tsoffin ƴan wasan ƙwallon kafa na Super Eagles da gwamnatin tarayya ta yi masu alƙawali.
Hotunan da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta wallafa a Twitter sun nuna lokacin da ƴan wasan ke karbar takardun gidajen hannun Fashola a ranar Juma’a.
An ba tawagar Super Eagles da suka buga wa ƙasar wasa a 1994 gidajen ne gidajen, bayan shekara 28 da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta yi masu alƙawali lokacin da ƴan wasan suka lashe kofin Afirka a Tunisia.