Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin “shugaba na gaskiya, dan’uwa kuma abokina” wanda ya nuna “hankalin manufa, natsuwa, da balaga” a makonnin da suka gabata a Babban Taron Jam’iyyar.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya bayyana cewa yabon Tinubu na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun jigon jam’iyyar APC.
Tinubu ya nuna jin dadinsa ga wasikar taya murna da shugaban kasar ya aike masa, inda ya kara da cewa, duk da cewa duk ’yan takarar sun yi tsammanin shugaba Buhari zai “zaba” wanda zai gaje shi, sai kawai ya kyale su..
Ya taya shugaban kasar murnar kammala babban taron cikin nasara tare da ba shi tabbacin wani batu da ya mayar da hankali wajen yakin neman zabe wanda zai kai ga zaben 2023.