Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Lahadi ya bayyana cewa, wasu mutane sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada daya daga cikin masu neman shugabancin kasar a matsayin dan takarar jam’iyyar amma shugaban ya ki amincewa.
Tinubu a wata sanarwa da ya fitar ta ofishin yada labaransa mai dauke da sa hannun Mista Tunde Rahman, ya ce, rawar da shugaban kasa da gwamnonin APC na Arewa suka taka na cewa dole ne a bar duk masu neman shugabancin kasar nan zuwa filin daga ya tabbatar masa da cewa Najeriya za ta iya tsira da hadin kai da kalubalensa.
Kwana daya kafin a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdulahi Adamu ya yi taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar ya sanar da shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmed Lawan a matsayin zababben dan takarar jam’iyyar.
Sai dai sauran ‘yan jam’iyyar NWC da gwamnonin APC na Arewa sun dage cewa dole ne a bar duk masu neman shugabancin kasar su fita filin daga.
Sai dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC wanda ya gabatar da shirinsa na aiki ga shugabannin Afenifere, yayin da yake jawabi a gidan Pa Reuben Fasoranti a ranar Lahadi a Akure, ya ce shugaba Buhari da gwamnonin APC na Arewa sun tabbatar masa da cewa Najeriya za ta iya tsira daga hadin kan ta da kalubalen da take fuskanta. .