Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bi sahun ‘yan uwa, abokai da abokan arziki wajen alhinin rasuwar tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Mustapha Balogun.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina ya aike a ranar Juma’a a Abuja, shugaban ya kuma jajanta wa rundunar ‘yan sandan Nijeriya, wata cibiya ta Balogun ya kwashe tsawon rayuwarsa yana aiki.
Buhari ya tuna cewa, Balogun, a lokacin da yake rike da mukamin IGP, ya yi iya kokarinsa wajen ganin ‘yan sanda sun yi aikin da ya kamata a tsarin dimokuradiyya.
Ya kuma ce, bajintar da Balogun ya yi na kara kwarin gwiwar jami’ai da maza a cikin rundunar wadanda suka yi aiki a karkashinsa sun amince da shi.


