An karrama zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, lambar girma mafi girma a Najeriya, Grand Commander of the Order of the Federal Republic, GCFR.
Haka kuma, an yiwa zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Settima shima an karrama shi a matsayin Grand Commander of the Order of the Niger, GCON.
Buhari ya karrama su ne yayin gudanar da taron a Aso Villa Abuja.
A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya mai jiran gado, wanda zai gaji shugaba Muhammadu Buhari.