Shugaban kasa, Muhammadu Buhari,ya bada tabbacin gwamnatin tarayya za ta karbe jami’ar kimiyar lafiya ta Uburu, Ebonyi tare da sarrafa ta a matsayin jami’ar likitanci ta tarayya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen wani liyafar cin abincin dare da aka yi masa a ranar Alhamis a Abakaliki, bisa bukatar farko da gwamna David Umahi na Ebonyi ya gabatar.
Jami’ar dai tana karamar hukumar Ohaozara ne a jihar.
Shugaban ya shaida wa al’ummar Ebonyi cewa, an fara aiwatar da shirin sauya mallakar jami’ar kuma ‘’ za a kammala shi nan ba da jimawa ba.
A kan bukatar da gwamnan jihar ya yi na sayen kayan aikin filin jirgin da kudinsu ya kai Naira biliyan 10, shugaban ya yi alkawarin gano matsayin ma’aikatar sufurin jiragen sama dangane da hakan.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, wadannan cibiyoyi da ma sauran su za su kara kaimi wajen bunkasar tattalin arzikin jihar musamman ma kasa baki daya.
Buhari wanda ya baiwa gwamnati da al’ummar Ebonyi tabbacin goyon bayan gwamnatinsa, domin baiwa gwamnan damar cimma burinsa na jihar, ya gode musu bisa tarbar da aka yi masa a ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar.