Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sallami hadimar mai dakin sa Asiha Buhari, wato Zainab Kazeem, wacce ita ce mataimakiya na musamman ga shugaban kasa bangaren ayyukan gida da taruruka, daga aiki.
Buhari ya kuma amince da nadin Muhammad Sani Zorro, dan jarida, dan siyasa kuma tsohon dan majalisa a matsayin hadimin shugaban kasa a bangaren harka da al’umma da tsare-tsare, a ofishin First Lady.
An kuma yi wa wasu mutane uku canjin wurin aiki,ciki akwai Dr Muhammad Kamal Abdulrahman, Hadi Uba, da Wole Aboderin.
Sabon nadin da korar na cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter.