Shugaban kasa, Muhammadu Buhar,i ya amince da bai wa Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno lambar girmamawar kasa ta CON (Commander of the Order of the Niger).
Wata sanarwa da Mallam Isa Gusau, mai magana da yawun gwamnan jihar Borno ya fitar ta ambato ministan ayyuka na musamman da harkoki tsakanin gwamnatoci, Sanata George Akume na yi wa Farfesa Umara Zulum wannan albishir.
Ministan ya ce sai ranar Talata 11 ga watan Oktoba za a yi bikin ba da lambar girmamawar ta kasa a Abuja.
A bara ma, shugaban kasar Nijar Mohammed Bazoum ya bai wa Gwamna Zulum lambar karramawa ta kasar ta “de Grand Officer Dans I`Ordre”.