Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙwancin shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo a babban birnin Tarayya a yau Alhamis.
Shugaban na Ghana ya halarci bikin cika shekara 20 da kafa cibiyar Shehu Musa Yar’Adua a Abuja.
Bikin ya samu halartar tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar.