Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da shirin tattalin arziki na fasahar intanet.
Shugaban ya kaddamar da wannan shirin ne karkashin ministan sadarwar da tattalin arziki ta fasaha, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, wanda shi zai jagoranci shirin.
Shirin ya kunshi wani kwamitin mambobi da Buhari ya kaddamar da za su ke wannan aiki, wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ta wannan fanin.
Shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da bada ƙaimi a fanin fasahar intarnet, domin samun ribar fasahar zamani domin cigaban tattalin arzikin Najeriya. In ji BBC.