fidelitybank

Buhari ya kaddamar da aikin hako man fetur a Bauchi

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Lokacin ƙaddamarwar shugaba Buhari ya umurci kamfanin mai NNPCL ya yi duk mai yiwuwa a hurumin da doka ta ba shi, domin tabbatar da sun janyo masu zuba jari domin bunƙasa sarrafa man fetur a Arewacin Najeriya.

Haka kuma Shugaba Buhari ya ce ya tattauna da gwamnonin Bauchi da Gombe, inda suka tabbatar masa da za su bayar da haɗin kai domin ci gaba da aikin bunƙasa haƙo man fetur ɗin.

Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan ƙaddamarwa, BBC ta tattauna da ɗaya daga cikin manyan jami’an kamfanin mai na NNPC da ke kula da inda kamfanin ke zuba jari, Bala Wunti, inda ya shaida wa BBC cewa an gano aƙalla ganga fiye da biliyan ɗaya ta ɗanyen man fetur a ƙarƙashin ƙasa.

Kazalika ya ce ana fatan gina matatar mai da kamfanonin samar da taki da kuma iskar gas.

Matatar man da ake fatan ginawa za ta riƙa sarrafa ganga fiye da 100,000 a kullum.

legitnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe ƴan ɗaurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...
X whatsapp