Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ,ya kaɗa ƙuria’a mazaɓarsa da ke garin Daura da ke jihar Katsina.
Shugaban wanda ya fito da misalin ƙarfe 9:30 na safe ya kaɗa ƙuri’ar tasa ne tare da mai ɗakinsa A’isha Buhari.
Muhammadu Buhari na kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas a wannan shekara, inda ake sa rana zai miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.