Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jajanta wa takwaransa na Koriya ta Kudu Yook Sukyeol game da hatsarin mutuwar mutum 153 a wurin bikin Halloween.
“Ina addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata,” in ji Buhari – wanda ya koma gida daga Koriyar a ranar Juma’a – cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga Shugaba Yoon…Najeriya na jimami tare da ku a wannan lokaci na juyayi,” a cikin saƙon na Buhari.
Baya ga 153 da suka mutu, wasu 82 sun ji raunuka daban-daban sakamakon turereniyar da mahalarta bikin na shekara-shekara suka yi ranar Asabar a Seoul babban birnin ƙasar.
Hukumomi sun ce akasarin waɗanda abin ya shafa ‘yan ƙasa da shekara 20 ne da ɗoriya.