fidelitybank

Buhari ya jajanta wa Jonathan

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan bisa rasuwar ma’aikatan sa guda biyu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.

Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bi sahun ‘yan kasar wajen addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Shugaba Buhari ya bukaci iyalansu da su kalli rasuwarsu a matsayin sadaukarwa ga kasa.

Shugaban wanda ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sa Shugaba Jonathan ya tsira daga hatsarin, ya bukace shi da kada ya shagaltu da tafiye-tafiyen da yake yi a cikin gida da waje da ya shafi samar da zaman lafiya a gida da waje.

Aminiya ta ruwaito yadda ayarin motocin Jonathan suka yi hatsari a kusa da filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja.

Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaban kungiyar matasan kabilar Ijaw na kasa, Peter Timothy Igbifa, ya yi zargin cewa, hatsarin wani shiri ne da wasu makarkashiya suka shirya don kawo karshen rayuwar tsohon shugaban kasar gabanin babban zabe na 2023.

A cewarsa, ‘yan sandan sun yi amfani da kansu ne a matsayin garkuwar dan Adam wajen kare Jonathan kuma a cikin haka ne suka biya farashi mai tsoka.
Ya yi barazanar cewa, matasan Neja-Delta za su durkusar da tattalin arzikin kasar idan wani sharri ya samu Jonathan.

Sai dai hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta shaida wa Aminiya cewa “gudu” ne zai iya haddasa hadarin.

Kwamandan hukumar dake kula da reshen babban birnin tarayya Abuja, Samuel Ogar Ochi, ya ce an fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp