fidelitybank

Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron majalisar tsaro ta ƙasa a Abuja a yau Laraba.

An tattauna kan batutuwa da dama musamman ma kan tsari na tsaro da hukumomin tsaro suka yi gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

A lokacin da yake tattaunawa manema labarai bayan taron, sufeton ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da zaɓen da ke tafe.

Ya ce sun tanadi matakan tsaro da dama domin ƙare lafiyar waɗanda za su kaɗa kuri’a, inda ya buƙace su da su fito ba tare wata fargaba ba domin zaɓar wanda suke so.

Ya ce sun kuma faɗa wa shugaban ƙasa cewa yanayin tsaro na kyautata a Najeriya.

Shi ma da yake magana bayan kammala taron majalisar tsaron, ministan shari’a kuma babban attoni janar na ƙasa, Abubakar Malami, ya ce abin da ya sa gwamnatin tarayya ta kira wannan taro shi ne domin ji daga hafsoshin tsaron ƙasar da shugabannin sauran hukumomin tsaro kan irin shirin da suka yi gabanin zaɓe da ke tafe.

Ya ce bayan ji daga garesu, gwamnati ta yi na’am da irin shirye-shiryensu, inda ya ce gwamnatin ta tanadi duk abin da ya kamata wajen ganin a samu nasarar gudanar da zaɓukan lami lafiya.

Manyan jami’an gwamnati da dama ne suka halarci taron.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp