Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jaddada alkawarinsa na tabbatar da an yi zaben da babu cuta babu cutarwa a cikinsa a kasar, wanda kuma aka yi yarjejeniyar duka ‘yan takarar za su amince da sakamakon zaben.
Cikin wata sanarwa da kakakin Shugaban Malam Garba Shehu ya fitar ya ce, Shugaba Buhari ya bayyana matsayinsa a birnin Washinhton na Amurka a wata tattaunawa da ya yi mai taken, “Tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya”.
Shugaba Buhari yace “tun daga shekarar 2015, yadda muke gudanar da zabenmu na kara habbaka a hankali.
“Daga zaben 2019, zaben maye gurbi da kuma na karshen lokaci da aka yi a Edo da Ekiti da Anambra da kuma Osun an yi su cikin yanayin gamsuwa daga bangaren masu takara da wadanda suka yi zaben.
“Haka kuma muke fata a 2023. duk da cewa matakin masu sanya ido na duniya zai kara karfafawa ‘yan siyasa amincewa da sakamakon zaben.”
Da yake amsa tambya game da shirin INEC na zaben 2023, shugaba Buhari ya ce “INEC a shirye take saboda mun basu duk wani abu da uke bukata wanda suka tambay saboda ba na son wani uzuri kan cewa gwamnati ta hana su kudi, domin haka ba ta da wani uzuri.”