Wani dan Majalisar dokokin tarayya, Sani Bala Tsanyawa, ya ce, akwai guraben aikin gwamnatin tarayya sama da dubu ɗari da ashirin amma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya hana a cike su.
Honorabul Sani Bala Tsanyawa, wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da Ayyukan gwamnati na Majalisar Wakilan Najeriya ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da BBC Hausa.
Ya ce tun a shekarar 2019 ne Shugaba Buhari ya sanar wa majalisar dokoki ɗaukar matakin a lokacin da ya je zaurenta domin gabatar da kasafin kuɗi.
A cewarsa “Lokacin gabatar da kasafin kuɗi da (shugaban kasa) ya kawo wa majalisa, yake faɗa cewa ya dakatar da ɗaukan aiki a ‘mainstream civil service’ – wato ma’aikatan da ke a aiki a ma’aikatu na kwaryar aikin gwamnati.”
Ya ce tun da shugaban ƙasar ya sanya wannan haramci ba a ƙara ɗaukar aiki ba a irin waɗannan ma’aikatu.
Sai dai a cewarsa an bai wa wasu ma’aikatun gwamnatin damar daukar ma’aikata saboda dalilai masu ƙarfi.
Bangarorin da aka yi wa rangwamen sun haɗa da na tsaro da lafiya – sakamakon barkewar annobar korona.
Ya kara da cewa “Daga shekara biyar a baya zuwa yau, bincikenmu ya nuna cewa ma’aikata dubu ɗari da talatin ne suka bar aiki.”
“Wasun su ko dai sun mutu, wasu kuma sun yi ritaya, wasu kuma sun samu wani aikin na daban sun bar na gwamnatin tarayya.”
Ya ce amma a tsawon waɗannan shekaru biyar bayan sanya haramcin, mutum dubu shidda da dari bakwai ne kacal gwamnatin tarayya ta ɗauka aiki. In ji BBC.
Sannan ya ce duk da haka har yanzu yawan guraben na kara yawa saboda a kodayaushe akan samu ma’aikatan da ke mutuwa ko ajiye aiki, to amma har yanzu ba a cire wannan haramci ba.
Sai dai ya ce, akwai wasu hukumomin da a wani lokaci sukan dauki ma’aikata, kamar babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar sadarwa ta kasa (NCC), amma ba a ma’aikatun kwaryar aikin gwamnati ba, waɗanda a turance ake kira ‘ministries’.