fidelitybank

Buhari ya halarci bikin tunawa da ‘yan Mazan jiya

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci bikin taron tunawa da ‘yan mazan jiya, wanda kuma shi ne na ƙarshe da shugaban ƙasar zai halarta a matsayinsa na shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin tsaro na ƙasar.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce wannan ne karo na takwas kuma na ƙarshe da Buhari ke halartar wannan biki a matsayinsa na shugaban ƙasa.

Daga cikin waɗanda suka halarci bikin wanda aka gudanar a Abuja babban birnin ƙasar sun haɗar da mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da babban alƙalin alƙalan ƙasar, Mai shari’a Olukayode Ariwoola, da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ana dai gudanar da wannan biki ne a duk shekara domin tunawa da irin gagarumar gudunmowar da tsoffin dakarun ƙasar suka bayar wajen zaman lafiya da ci gaban ƙasar.

A wajen bikin Shugaban ƙasar da sauran jami’an gwamnati kan ajiye furanni domin nuna jinjina ga ‘yan mazan jiyan, tare da yin faretin girmama wa ga shugaban ƙasa, sannan kuma shugaban ya saki fararen tattabaru suka tashi sama duk domin nuna tunawa da irin ƙwazon da ‘yan mazan jiyan suna nuna ga ƙasar.

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp