Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince da nadin karin hadimai biyu ga Aisha Muhammadu Buhari.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ƙasa Buhari, ya sallami daya daga cikin tsofaffin hadiman Aisha, sannan a ka yi wa wasu sauyin wuraren aiki.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, Buhari ya nada Aisha Rimi a matsayin babbar hadima ta musamman, sannan Dr Zabah a matsayin likitan Aisha Buhari.