Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci sabbin ministoci da su tuntubi tare da hada kai da tsofaffin takwarorinsu na majalisar tare da mai da hankali kan tafiyar da muhimman shirye-shirye da wannan gwamnatin ta riga ta fara.
Sabbin ministocin da aka nada da mukamansu sun hada da: Ikechukwu Ikoh, karamin ministan kimiyya da fasaha; Umana Umana, ministan harkokin Neja Delta; Udi Odum, Karamin Ministan Muhalli da Ademola Adegoroye, Karamin Ministan Sufuri;
Sauran su ne; Umar El-Yakub, karamin ministan ayyuka da gidaje; Goodluck Opiah, Karamin Ministan Ilimi da Nkama Ekumankama, Karamin Ministan Lafiya.
Shugaban ya kuma sake nada Sen. Adeleke Mamora, ministan kimiyya da fasaha (tsohon karamin ministan lafiya); Mu’azu Jaji Sambo, Ministan Sufuri (Tsohon Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje); Sharon Ikeazor, Karamin Ministan Neja Delta (Tsohon Karamar Minista, Muhalli) da Sen. Gbemisola Saraki, Karamin Ministan Ma’adinai da Karfe (Tsohon Karamin Ministan Sufuri).
Ya kuma gargadi dukkan ‘yan majalisar ministocin kasar kan ayyukan cin hanci da rashawa, yana mai jaddada cewa dole ne jami’an gwamnati su kasance a sama, kuma wadanda aka kama da cin hanci da rashawa za su fuskanci fushin doka.