fidelitybank

Buhari ya gargaɗi sabbin shugabannin jam’iyyar APC karsu bari kuɗi ya rinjaye su

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi sabon kwamitin ayyuka na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa cewa, kada su bari ‘yan takara mafi karfin arziki su rinjaye su a zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Buhari ya yi wannan gargadin ne a babban taron jam’iyyar APC na kasa a shekarar 2022 da aka gudanar a Abuja, inda ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su rika inganta dimokuradiyyar cikin gida a kodayaushe da kuma daidaito ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu zabe da su inganta tsarin zabe, su kara nuna gaskiya, cike gibin da ake da su, sannan su kara kima ga dimokradiyyar Najeriya, domin dimokuradiyyar ta samu ci gaba.
Shugaban wanda ya bayyana dalilansa na sa baki a cikin al’amuran jam’iyyar a kwanakin baya, ya ce ba wai an yi hakan ne don danne muryoyin da ba su dace ba.

“Kwanan nan, na sami dalilin shiga cikin rikicin shugabancin da ke shirin kawo rudani a cikin jam’iyyar.Irin wadannan rigingimun cikin gida sun zama ruwan dare a cikin dimokuradiyya irin namu, amma dole ne mu guji zafafa harkokin siyasa, kada mu bari bambance-bambancen da ke tsakaninmu ya tsaga da kawo cikas ga jam’iyyar.

“Kamar yadda na fada a baya, ba ta amfanar kowa ko jam’iyya, idan mu a matsayinmu na shugabanni muka yi kasa a gwiwa, muka koma ga bata-kashi da suna a kafafen yada labarai. In ji Buhari.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp