fidelitybank

Buhari ya gana da gwamnonin Arewa a kan matsalar tsaro

Date:

Jim kadan bayan dawowarsa daga jihar Ebonyi, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da wasu gwamnonin Arewa da kuma shugabannin hukumomin tsaro a fadar shugaban kasa ta Villa Abuja.

Taron wanda ya gudana a bayan fage a zauren majalisar na fadar shugaban kasa, an fara shi ne da misalin karfe uku na rana.

Ba a bayar da cikakken bayani kan dalilan ganawar ba, sai dai majiyoyi daga fadar shugaban kasar sun ce, taron na da alaka da matsalar tsaro a kasar nan, musamman a Arewacin kasar nan.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Simon Lalong na Filato, Nasir El-Rufa’i na Kaduna, Abdullahi Ganduje na Kano, Aminu Tambuwal na Sokoto, Sani Bello na Niger, Abubakar Badaru na Jigawa, Umara Zulum na Borno, Atiku Bagudu na Kebbi da Bello Matawalle na Zamfara.

An tattaro cewa, duka gwamnonin Katsina da Yobe, Bello Masari da Mai Mala Buni, su ma ana sa ran halartar su a wajen.

Har ila yau, Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya jagoranci tawagar tsaro, ciki har da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya; babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; hafsoshin tsaro da shugabannin sauran hukumomin tsaro sun halarci taron.

Hafsan hafsoshin da suka halarci taron sun hada da babban hafsan soji, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp