Shugaba Muhammadu Buhari na ganawa yanzu haka da gwamnonin APC 22 gabanni zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban kasa da za a gudanar daga 6 zuwa 8 ga watan Yuni.
Daga cikin mahalarta taron har da shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
Gwamnan Kaduna kaɗai ne ya samu wakilcin mataimakinsa a taron da ake gudanarwa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Jaridun Najeriya na cewa ana gudanar da taron ne domin daldale abubuwan da suka kasance masu sarkakiya gabannin zaɓen fitar da gwani.
APC ta dage zaben fitar da ɗan takarar shugaban kasa da a baya ta tsara gudanarwa tsakanin 29 ga watan Mayu zuwa 30, zuwa 6 da 8 ga watan Yuni, bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta dage wa’adin fitar da ‘yan takara.
Ana saran shugaba Buhar ya tafi birnin Madrid na Sifaniya a wata ziyara kwanaki biyu bayan kammala ganawar


