fidelitybank

Buhari ya gana da fasinjojin jirgin ƙasa Kaduna

Date:

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya gana da wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan da ‘yan bindiga suka sace daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.

Shugaban kasar ya gana da mutanen ne ranar Alhamis a fadar Aso Villa da ke Abuja kwana daya bayan sako karin mutum biyar da aka sace a jirgin kasan.

Ko da yake kawo yanzu ba a bayyana batun da suka tattauna ba, amma hakan na faruwa ne makonni kadan bayan ‘yan bindigar sun sha alwashin sace shi kansa shugaban kasar da kuma gwamnan Jihar Kaduna Nasir Elrufai.

Sun yi barazanar sace shugaban kasar ne a wani bidiyo da suka fitar wanda ya nuna su suna lakada wa fasinjojin duka.

Har yanzu dai akwai sauran fasinjojin da ke hannun ‘yan bindigar, wadanda suka yi barazanar kashe su idan gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba.

Shugaba Buhari ya sha kakkausar suka daga wurin ‘yan kasa, bisa abin da suka kira rashin kubutar da fasonjojin duk kuwa da umarnin da ya bai wa jami’an tsaro na yin hakan.

A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne masu tayar da ƙayar baya suka kai wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari da daddare.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp