Shugaban kasa Muhamamdu Buhari, ya bude katafariyar Gadar Neja ta Biyu, domin saukaka wa masu tafiya garuruwansu zuwa bukukuwan karshen shekara cikin kwanciyar hankali.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda Ministan Ayyukan Babatunde Fashola ya wakilta, a ziyarar gani da ido, ya ce, an gina gadar ce daga kudaden da ake zargin an sace su daga kasar kuma aka boye a kasashen waje, wadanda aka karbo mafi yawan su daga Amurka.
Sannan ya ce, manufar gina gadar shi ne kare rayuka da magance talauci da ake fuskanta sakamakon yawan sa’o’in da ake dauka a cinkoson da ake samu a tsohuwar Gadar Neja.
Ya ce, yin gadar zai zama maras amfani idan masu amfani da ita suka zabi tukin ganganci da ka iya zama barazana ga rayuwarsu.
Ministan ya kuma ce, da an tsara a bude ta a ranar !4 ga watan Disamba amma saboda wasu dalilai suka sa aka daga zuwa 15 ga watan Janairun 2023.