Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya bukaci majalisar wakilai ta amince da Naira Tiriliyan 4, domin samar da tallafin man fetur.
Bukatar shugaba Buhari na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ya karanta yayin zaman majalisar.
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin ta ce, ana bukatar Naira Tiriliyan 3, domin biyan tallafin a shekarar 2022.
Shugaban kasa ya bukaci ‘yan majalisar su kara ma’aunin man fetur daga dala 62 zuwa dala 73 kan kowacce ganga.
Sai dai a cikin wasikar da Mista Gbajabiamila ya karanta, Shugaban Buhari, ya ce, Naira tiriliyan 3 ba za ta wadatar ba, saboda karin farashin danyen mai wanda a halin yanzu ya kai dala 100 kan kowacce ganga.