A karo na biyu cikin kwanaki biyu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shiga cikin ayarin gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023, Bola Tinubu a ranar Talata a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Shugaban ya isa yankin Arewa maso Gabas ne a ranar Litinin din da ta gabata inda ya kaddamar da ayyuka takwas na gwamnatin tarayya da na jiha a Yobe, mahaifar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
Gwamna Mai Mala Buni ya karbi bakoncin Buhari a Yobe tare da wasu jiga-jigan APC. Shugaban ya halarci taron gangamin shugaban kasa na jam’iyyar APC a Yola, babban birnin jihar Adamawa ranar Litinin.
A taron da aka yi a Yobe ranar Talata tare da shugaban kasa akwai Lawan, Buni, Tinubu; abokin takararsa Kashim Shettima; da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu.
Sauran wadanda suka halarci gangamin akwai Gwamna Simon Lalong (Plateau); Babagana Zulum (Borno), Badaru Abubakar (Jigawa), Atiku Bagudu (Kebbi) da Inuwa Yahaya (Gombe).
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya ce Buhari zai shiga yakin neman zaben Tinubu a jihohi 10.