Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa jam’iyyar APC ta mayar wa da duk wani ɗan takara da ya hakura da neman mukami kudinsa.
A ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022, Punch ta rawaito cewa, shugaban kasa ya na umartar APC ta mayar da kuɗaɗen ƴan takarar da suka biya kuɗin fam.
Wasu ‘yan siyasa sun fasa takara, sun yarda su janyewa abokan hamayyarsu. Don haka Muhammadu Buhari ya hana APC taba irin wadannan kudi.
Haka zalika, Mai girma Buhari ya fadawa gwamnonin jam’iyyarsa da su yi kokari wajen ganin an zabi sababbin shugabannin APC na kasa ta hanyar maslaha.
Shugaban Buhari ya baiwa gwamnoninsa nan da sa’o’i 24, su fito da sunayen wadanda ake so su rike duk wasu mukamai na kasa a jam’iyyar APC mai mulki.