Jagorar jam’iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce, tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Muhammadu Buhari ya hore shi da riƙe amanar talakawan ƙasar.
Yayin da yake jawabi a wajen ta’aziyar rasuwar Buhari a garin Daura, mahaifar marigayin, Peter Obi ya ce yana tuna kalaman da Buhari ya faɗa masa lokacin da yake raye.
”A lokacin da nake yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, na kai masa ziyara, kuma kiran da ya yi min shi ne, ya ce Peter ka kula da talakawan Najeriya, ni kuma na faɗa masa wannan shi ne babban muradina”.
Peter Obi ya ce babban abin da shugabanni za su koya daga halin Buhari shi ne sauƙin kansa.