Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya baiwa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu damar lashe zaben shugaban kasa da ya gabata.
Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya ce dalilin da ya sa Tinubu ya fara kai wa shugaban kasa takardar shaidar cin zabe a Daura, jihar Katsina.
Da yake magana a gidan talbijin na Najeriya, NTA, Shehu ya ce: “Shi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Tinubu damar yin nasara cikin gaskiya da adalci.
“Lokacin da Tinubu ya karbi satifiket dinsa daga hannun INEC, abu na farko da ya yi shi ne ya tashi zuwa Daura ya nuna wa shugaban kasa.
“Shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu baya gajiyawa da fadin cewa shugaban kasa ya bashi damar yin nasara. Yana da matukar muhimmanci. Ya ba shi damar yin nasara cikin gaskiya da adalci.”


