fidelitybank

Buhari ya amince da siyan motoci masu sulke 400

Date:

Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya amince da sayo motocin yaƙi masu sulki 400 ga dakarun soji, domin kare babban birnin ƙasar Abuja da jihar Nasarawa da wasu yankuna na jihar Niger.

Sabon babban kwamandan rundunar soji mai lura da yankin Manjo Janar Mohammed Usman,ne ya bayyana haka ranar Laraba a cikin jawabin godiya da ya gabatar jim kaɗan bayan shugaba Buhari ya yi masa ƙarin girma.

Manjo Janar Usman ya gode wa shugaban ƙasar saboda jajircewarsa da taimakon da ya ke bai wa rundunar, ciki har da amincewa da sayo motocin sulken 400, waɗanda ya ce sun isa wajen kare yankinsa da ya ƙunshi babban birnin ƙasar, da jihar Nasarawa da kuma wasu yankunan jihar Niger.

Haka kuma ya bayyana jin daɗinsa game da ƙarin girman da aka yi masa, yana mai cewa hakan zai taimaka masa wajen gudanar da aikinsa.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gobara na cigaba da lakume wasu yankunan Turai

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan...

An kama Fursunoni 7 da suka tsere daga gidan kurkukun jihar Nasarawa

Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce...

Gwamnati za ta gina titin jirgi a jihohi shida

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta haɗa gwiwa da...

Tinubu ya na cikin koshin lafiya – Farouk Adamu Aliyu

Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Faruk Adamu...

Amurka ta saka ladan dala miliyan biyar a kamo jagoran ‘yandaban Haiti

Amurka ta sanya dala miliyan biyar a matsayin lada...

Gwamnati ta janye karar da ta shigar kan Fasinjar jirgin Ibom

Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar kan...

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...
X whatsapp