fidelitybank

Buhari ya amince da nada Sarkin Kano a matsayin Uban Jami’a

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Uban jami’ar Calabar ta jihar Cross River.

Shugaban Jami’ar, Janar Matthew Luther Agwai mai ritaya ne ya bayyana hakan, a ranar Laraba, a lokacin da ya jagoranci ‘yan majalisar zuwa ziyarar taya murna da suka kai wa Sarkin a fadarsa.

Agwai ya ce”Al’ummar Jama’ar Calabar ta cika da murna da nadin da a ka yi wa Sarki Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Uban Jami’ar. Dimbin gogewar Sarkin, jami’ar za ta samu babban matsayi na ilimi”.

Da ya ke mayar da martani, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin tarayya da ta same shi da ya cancanci zama Uban Jami’ar.

“Muna tattaunawa da jami’ar Calabar da ke jihar Cross River, kuma za mu yi iya kokarinmu wajen ganin an samu nagartaccen Ilimi.” A cewar Alhaji Aminu Ado Bayero.

Sarkin ya nemi goyon bayan daukacin ‘yan Majalisar da na Jami’ar wajen ganin an cimma burin da a ke so.

Daga nan sai ya yaba da namijin kokarin da Shugaban Jami’ar, Janar Matthew Luther Agwai, da ‘yan uwa na Jami’ar su ka yi, inda ya bukace su da su ci gaba da gudanar da aikin.

www.leadership ng.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp