fidelitybank

Buhari shugaba ne mai gaskiya da rikon amana tare da tausayin Talaka – Garba Shehu

Date:

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya kasance mutum mai gaskiya da amana da tausayin talakawa.

Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar da tsohon shugaban yake murnar cika shekara 82 a rayuwarsa.

Garba Shehu ya ce, “Buhari shugaba ne daban, wanda yake damuwa da damuwar talakawa da masu rauni, sannan yake dagewa wajen inganta rayuwar talakawa da fitar da su daga cikin ƙunci.”

Garba Shehu ya ce siyasa da cin hanci da rashawa ɗanjuma ne da ɗanjumai a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya. “Tunanin mutane shi ne duk ɗansiyasa ɗan rashawa ne. Amma shi sunansa “Mai gaskiya” saboda gaskiyarsa da rashin ɗaukar duniya da zafi.”

Garba Shehu ya ƙara da cewa Buhari ya yi kamfe ne kan inganta tattalin arziki da samar da tsaro da yaƙi da rashawa.

“A zamanin mulkinsa, ƙasar ta ga yadda aka ɗauki matakai masu yawa domin yaƙi da talauci. Buhari ya mayar da hankali kan inganta kiwon lafiya, inda a zamaninsa aka cire ƙasar daga cikin masu fama da cutar polio,” in ji shi.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp