fidelitybank

Buhari ne ya hana EFCC ta bincike ni – Osinbajo

Date:

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hana shi neman hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta binciki zargin zamba da ake yi masa.

Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan shirin bada agajin gaggawa da bala’o’i a shekarar 2018 ya tuhumi hukumar gudanarwar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA.

Hukumar wadda Osinbajo ke shugabanta, an zarge ta da amincewa da wani asusun shiga yankin arewa maso gabas na Naira biliyan 5.8 ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma a shekarar 2020, an zargi mataimakin shugaban kasar da karbar Naira biliyan 4 daga hannun Ibrahim Magu, tsohon shugaban riko na EFCC.

Osinbajo ya bayyana ikirarin a matsayin “marasa tushe” kuma ya bukaci tsohon sufeto-janar na ‘yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya binciki zargin.

Da yake magana a ranar Juma’a a wani liyafar cin abinci na sirri don murnar cikar Buhari shekaru 80, Osinbajo ya ce: “Wata rana na je wurinsa saboda akwai wasu zarge-zarge da aka yi mini.

“Na je wurinsa ne domin in nuna masa wasikar da na rubuta wa EFCC domin ta bincika.

“A wannan lokacin ya ce, ‘VP, me yasa kuke damuwa da duk waɗannan mutanen? Wadannan mutane dai suna ta zarge-zarge iri-iri, suna ta yada labarai iri-iri, har ma suna cewa wai zan kara aure. Kuma har wasu wawayen mutane suna jira a Masallacin kasa, suna jira in zo in kara aure,” inji Osinbajo.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...

Gwamnatin Kano ta gargadi Matasa da ‘yan Gwangwan kan sayen kayan gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa...

NIMET ta gargai Borno kan ambaliya da sauran jihohi

A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya...

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...
X whatsapp