Shugaban kasa Muhammmadu Buhari na jagorantar taron Majalisar Magabata da ke tattauna muhimman batutuwan da kasar ke fama da su a yanzu musamman na sauyin kudi da zabe.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mahalatta taron a fadarsa da ke Abuja akwai tsofaffin shugabannin kasar da suka hada da Goodluck Jonathan da Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar da kuma Olusegun Obasanjo da ke halarta ta intanet.
A wurin taron akwai kuma Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila.
Su kuwa gwamnonin jihohi da ke wurin sun hada da Nasir El-Rufai na Kaduna da Darius Ishaku na Taraba da Babajide Sanwo-Olu na Lagos da kuma Babagana Zulum na Borno.
Wasu gwamnonin da ke halartar taron ta intanet sun hada da Ademola Adeleke na Osun da Abubakar Badaru na Jigawa da Yahaya Bello na Kogi da Atiku Bagudu na Kebbi da Dapo Abiodun na Ogun da Aminu Tambuwal na Sokoto da Simon Lalong na Filato da kuma mataimakan gwamnonin jihar Nasarawa da Bauchi.
Ministan Abuja Mohammed Bello da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma Babban Lauyan gwamnati da Ministan Shari’a Abubakar Malami da kuma Gwamnan Babban Bankin kasar Godwin Emefiele na wurin taron.
Shugaban hukumar zaben Najeriyar, INEC, Mahmood Yakubu wanda shi ma yake zaurn taron ana sa ran zai yi wa majalisar bayani kan shirye-shiryen zabukan da za a fara ranar 25 ga watan nan na Fabarairu.
Dukkanin shugabannin tsaro na Najeriyar kamar yadda tashar talabijin ta Channel ta ruwaito suma suna halartar taron a fadar shugaban kasa.