Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana magabacinsa Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai kamala kuma mai gaskiya.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakin sa, Cif Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Asabar, yayin bikin murnar cikar tsohon shugaban kasar shekaru 81 a duniya.
Shugaba Tinubu ya jinjinawa irin jagoranci da kuma nasarorin da tsohon shugaban ya yi, inda ya tuna irin hidimar da ya yi wa kasa a lokuta daban-daban a matsayinsa na shugaban kasa da kuma na farar hula.
Ya kuma bayyana Buhari a matsayin mafi kyawun tsarin sadaukarwa, sadaukarwa, kishin kasa, rikon amana ga kasa.
“Shugaba Buhari ya fito daga cikin jiga-jigan shugabanni masu nagarta. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa kasa hidima, har ma ya samu kansa a tsare saboda kishin kasa da hidimar da yake yi wa kasarmu ta Uba.
“Fitowar shugabanni irin na abokina, Buhari, yana faruwa ne kawai ta hanyar tsararru na Ubangiji. Mutum ne mai cikakkiya kuma maras misaltuwa “in ji shugaban.