fidelitybank

Buhari ka yi daidai da ka ɗage ƙidayar 2023 – Ortom

Date:

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya yaba wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kan abin da ya kira sauraron koken jama’a ta hanyar ɗage ƙidayar jama’ar ƙasa ta 2023.

A tsakiyar wannan wata ne dai gwamna Ortom ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ɗage shirin ƙidayar jama’ar ƙasar har sai an samu ingantaccen zaman lafiya da tsaro a ƙasar.

A cikin wata sanarwar da mai bai wa gwamnan shawara kan kafofin yaɗa labarai Terver Akase ya fitar, gwamnan ya ce yin ƙidayar zai harfar da rashin adalci ga miliyoyin mutanen da rikice-rikice ya raba da muhallansu, kuma suke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar da ma faɗin ƙasar baki-ɗaya.

Karanta Wannan: Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya dakatar da ƙidayar Jama’a da Gidaje

Yayin da yake yabawa da matakin ɗage ƙidayar, gwamna Ortom ya ce “bayan ɗage ƙidayar ya kamata gwamnatin tarayya ta yi ƙoƙarin ƙwato garuruwa da mutanen da ke hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Ya ƙara da cewa dole a sanya rayuka da walwalar jama’a, sama da komai da ƙasa ke son yi don ci gaban al’ummarta

Da safiyar ranar Asabar ne dai hukumar ƙidayar ƙasar ta fitar da sanarwar ɗage ƙidayar bayan wata ganawa da jagororin hukumar suka yi da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ranar juma’a da maraice a fadarsa.

Sanarwar ba ta yi ƙarin haske a kan dalilan da suka janyo dakatar da ƙidayar ba, kwana huɗu kafin a fara fara ta.

Shugaba Buhari ya umarci hukumar ta ci gaba da shirye-shiryen da ta fara na ƙidayar 2023, domin kada a watsar da ƙoƙarin da aka faro, ta yadda gwamnati mai zuwa za ta samu bayanan da suka kamata don sauƙaƙa mata cimma burin wannan shiri.

An dai kashe maƙudan kuɗaɗe, kuma an shafe tsawon lokaci ana shirye-shirye don wannan gagarumin aiki.

Babu wani tabbaci a kan takamaiman lokacin gudanar da ƙidayar jama’a ta gaba a Najeriya, duk da yake bisa ƙa’ida kamata ya yi a yi aikin shekara bakwai da ta wuce.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp