Majalisar Wakilai, ta yi kira ga Shugaban Ƙasa, Mhammadu Buhari, ya yi amfani da dukkan ƙarfinsa wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar sassan ƙasar.
Majalisar ta yi kiran ne cikin wata matsaya da ta cimma yayin zamanta na yau Laraba.
Babu bayani kan ko sau nawa majalisar ta yi irin wannan kira yayin da gwamnatin ke cewa tana bakin ƙoƙarinta.
Wani rahoto kan sha’anin tsaro da kamfanin Beacon Consulting ya fitar ya ce hare-haren ‘yan bindiga sun kashe mutum 1,500 cikin watan Maris kaɗai a Najeriya.
‘Yan bindiga ƙarƙashin ƙungiyoyi daban-daban kan kashe mutane ko kuma yin garkuwa da su don neman kuɗin fansa a lungu da saƙo na ƙasar.