Wata kungiyar magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kebbi, ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyyar na kasa Sen. Abdullahi Adamu, da su shiga cikin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar.
Kungiyar, Concerned APC Members/Supporters in Aliero/Gwandu/Jega Federal Constituency, ta yi kira a cikin wata sanarwa da ta fitar a Birnin Kebbi ranar Alhamis.
Shugaban kungiyar Usman Ibrahim da Sakatare Mohammed Aliyu ne suka sanya wa hannu.
Kungiyar ta bayyana cewa, ficewar da manyan ‘ya’yan jam’iyyar APC ke yi zuwa wasu jam’iyyun siyasa a jihar na iya yin tasiri a zaben 2023.
Kungiyar ta kuma gargadi wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar kan hukunce-hukuncen da ba su dace ba tare da nuna alhini da rigingimun da ke faruwa a jam’iyyar.