fidelitybank

Buhari ka tsoma baki a kan ƙarin kuɗin makaranta – Ƙungiyar Ɗalibai

Date:

Ƙungiyar Ɗalibai ta ƙasa NANS, ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi ”gaggawar sa baki” game da ƙarin kuɗin makaranta da jami’o’in ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin ƙasar”.

Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa ”duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari”,

A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu daga cikin jami’o’in ƙasar suka bayyana ƙarin kuɗin makaranta.

To sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.

Dalilin ya da sa kenan suka rubuta wasika ga shugaba ƙasa, inda suka buƙace shi a matsayinsa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya.

Wasu jami’o’in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun nasu.

To sai dai ƙungiyar ta ce kundin tarin mulki ya wajabta wa gwamnati samar da ingantaccen ilimi ga ‘yan ƙasa, don haka dole ta samar da kuɗin gudanar da ɓangaren ilimi.

Buhari ya kashe Ilimi zamu yi jana’izarta – NANS

Haka kuma Sakataren na NANS ya ce, ”matuƙar ba a soke ƙarin kuɗin makarantar da aka yi ba, to kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na ɗaliban ƙasar ba za su koma makaranta ba, saboda ba za su iya biyan wannan kuɗi ba”.

Abin da kuma a cewarsa zai ƙara yawaitar masu aikata miyagun laifuka a fadin ƙasar saboda rashin makoma da ɗaliban ke da shi.

Mista Kankia ya kuma yi gargaɗin cewar ”matukar buƙatarmu ba ta biya ba, to za mu gudanar da gagarumar zanga-zangar da za ta shafi abubuwa da dama a faɗin kasar nan”.

yola news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp