Kungiyar koli da al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kada ta yi watsi da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice.
Ohanaeze ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tsoma baki a shari’ar Ekweremadu, ta mika ta zuwa Najeriya.
Ekweremadu da matarsa na fuskantar shari’a bisa zargin satar sassan jiki a kasar Ingila.
Ana zargin tsohon shugaban majalisar dattawan ne da shigo da wani dan Najeriya kasar Birtaniya da nufin yanke masa koda.
An so a yank kodar a dasa wa diyar Ekweremadu.
Sai dai babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya ce, gwamnatin Najeriya ba za ta tsoma baki a shari’ar Ekweremadu ba.


