Tsohon Gwamnan Soja na Jihar Kaduna, Kanar Abubakar Dangiwa Umar (rtd) ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta dakatar da shirinta na gudanar da kidayar jama’a a watan Afrilun 2023.
Kanar Umar (rtd) wanda shi ne shugaban kungiyar Movement for Unity and Progress (MUP) ya bayyana rahoton da aka yi na kidayar jama’a a matsayin abin ban tsoro.
Ya ce, Najeriya na fuskantar kalubalen da ke tattare da rashin tsaro da durkushewar tattalin arziki, Saboda haka fara kidayar jama’a zai zama wata barna da kuma barnatar da albarkatun kasa.