fidelitybank

Buhari ka gaggauta magance yajin aikin jami’o’i – Falana

Date:

Babban lauya kuma mai rajin kare dan-Adam Femi Falana ya bukaci Shugaban kasa, Muhammadu Buhar,i da ya mika kwarya-kwaryan kasafin kudi na Naira biliyan 200 da ake bukata na raya jami’o’in kasar, don kawo karshen yajin aikin malamansu.

Mr Falana, na ganin wannan zai taimaka gaya wajen kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in, abin da ya tsayar da harkokinsu tun watan Fabrairu.

Babban lauyan ya ce maganar da gwamnati ta yi cewa ba ta da kudin da kungiyar malaman jami’o’in kasar, ASUU ta bukata, ba magana ba ce, inda ya yi nuni da yadda gwamnatin ta shawo kan matsaloli irin na tallafin man fetur da kuma na bunkasa harkokin noma.

ASUU ta fara yajin aikin gargadi na mako hudu daga ranar 14 ga watan Fabrairu.

A ranar 14 ga watan Maris ta tsawaita shi da wata biyu domin gwamnati ta biya mata bukatunta, abin da bai samu ba.

Haka kuma ta kara zarcewa da mako 12, kamar yadda ta sanar ranar 9 ga watan Mayu.

Tun daga wannan lokaci kungiyar take yajin aiki, inda ta lashi takobin ci gaba da yi har sai gwamnati ta biya mata dukkanin bukatunta.

Bukatun da suka hada da, kyautata yanayin aikinsu da raya jami’o’in gwamnati da ba su ‘yancin cin gashin-kai da sauransu. A cewar BBC.

Wata babbar matsala daga cikin bukatun ita ce ta bayar da kudin farfado da jami’o’in wadanda suka kai kusan naira biliyan dubu 1.1.

Kudin da gwamnatin ta ce ba ta da shi tana mai nuni da faduwar farashin mai a lokacin wannan mulkin na Shugaba Buhari. Yarjejeniyar da aka kulla tun 2009.

Wata matsalar kuma ita ce ta amfani da tsarin musamman na biyan albashin malaman jami’o’in (IPPIS), wanda malaman suke ja a kansa.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp