‘Yan majalisar dattawan, sun nemi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar da aikin wutar Zungeru.
Kwamitin Majalisar kan Makamashi ne ya yi kiran bayan nazari a kan yadda aikin ke gudana.
Shugaban kwamitin, Sanata Gabriel Suswan, a yayin zaman kwamitin ya ce ba wai ba sa so a gudanar da aikin ba ne, tafiyar hawainiyar da aikin ke yi ne ta sa suka yanke wannan hukunci.
Ya ce, baya ga tafiyar hawainiyar da aikin ke yi babu kuma kayan aikin da ake bukata.
Sanata Suswan, ya ce a don haka suka bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aikin har sai samar da kayayyakin da ake bukata wajen gudanar da aikin samar da wutar lantarkin a Zungeru.
Kididdiga ta nuna cewa a tsakanin shekarar 2015 da 2022, babban layin da ke ba wa Najeriya wuta sau 98 ya na samun matsala, abin da ke jefa mutane da dama cikin duhu da kuma durkusar da harkokin kasuwanci a wasu sassan kasar.