Mai magana da yawun tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce babu wani rashin jituwa tsakanin mai gidansa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mal Garba Shehu, Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC game da wani littafi da zai kaddamar a yau Laraba kan irin yadda suka yi aiki da Shugaba Buharin mai taken “According to the President: Lessons from a presidential spokesman’s experience.”
Garba Shehu ya ce akwai jita-jita ce irinta mutane da yaɗ abubuwa da basu da tabbas a kai.
Da aka yi masa tambaya kan me ya sa Buhari baya hallatar taruka ko tsokaci kan wasu abubuwa na gwamnati sai Malam Garba Shehuu ya ce; “Buhari ba mutum ba ne me son shiga abin da bai shafe shi ba, sannan yana da dalilansa na wasu matakan da yake ɗauka idan aka tuntuɓemu za mu ba da amsa”.
Sannan game da littafin da ya rubuta ya ce yana ganin ya kamata mutane su fahimci wane ne Buhari da tsarin ayyukansa, ganin akwai mumunan fahimta da ake yi wa tsohon Shugaban.
Ya ce Allah ya ba shi damar aiki a fadar gwamnati, kuma tsawon shekarun da ya yi na aiki akwai darrusa da dama da suka koya da ya kamata na baya su sa ni.
Sannan matasa da masu karatun jarida akwai abubuwan koyo sosai daga rayuwar Buhari da ayyukansu a fadar gwamati.
Sannan littafi ya bayyana wane ne shugaba Buhari, tsarinsa da yanayin aikinsa, ganin ana yawaita samu masu kushe shi da cewa me ya yi a shekaru takwas da mulkinsa.
Littafi ya yi bayyani kan rayuwarsu ta Villa da fito da bayanai na gaskiya kan wasu zarge-zargen da aka rinka yi wa shugaban, kama daga batun tsaro, diflomasiyya da wasu batutuwa masu muhimmanci.
Ya ce karanta wannan littafi sai sake gamsar da al’umma fahimtar wane ne ainihn tsohon shugaba Buhari.
Sannan ko yanzu da aka ga yana kame jikinsa, kokari ne na ba wa kowa dama da kau da kai, saboda ba ya son shishigi kan wasu lamura da ba su shafe shi fa.