Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi bayanin dalilin da zai hana shi halartar taron kwamitin zartarwar jam’iyyar APC na ƙasa.
Ya ce ya aike wa jam’iyyar da saƙon neman uzuri don samun damar halartar wasu abubuwa da ya tsara yi kafin sanarwar taron.
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma jaddada goyon baya ga jam’iyyar da kuma fatan za a kammala taron lafiya.
Shi ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo ya aike da irin wannan saƙo na neman uzuri, kamar yadda mai magana da yawunsa, Laolu Akande ya sanar.
Akande ya ce Osinbajo baya ƙasar don haka ba zai samu halartar taron ba, kuma tuni ya sanar da jam’iyyar dalilansa.